Friday, July 8, 2011

Neman Gafarar Gwamnoni Uku Ga Boko Haram. (Tsakanin Sukar Lamiri Da Rusunawa Ga Karfi.)



                     Neman Gafarar Gwamnoni Uku Ga Boko Haram.

                                    Tsakanin Sukar Lamiri Da Rusunawa Ga Karfi.

                                                              (1-2)

                                                         Mujtaba Adam.
                                             nigeria3000@yahoo.com

8/7/2011


Yanzu duk shakiyyan birni sun fadi…. Ba tsoron Allah su ke ba, amma tsoron yari su ke yi. Saboda Allah na musu lamuni… yari ba ya bari sai can gaba.”
                                            
                           Ali Dan Sarki: Wakar Yarin Usumanu Nagoggo.


   (1)           


“Yin furuci da kuskure” kamar yadda Dmitri Fyodorovich, ya fadawa dan’uwansa Alyosha a cikin littafin Brothers Karamazov, “Abu ne mai tsarki.”  Wannan tsarkin na yin furuci da kuskure sannan  kuma da neman gafara akansa, ya samo asali ne daga kasantuwarsa wata kima ta ‘‘yan’adamtaka da addini da kuma lafiyayyen hankali.


Laifukan da su ke bijirowa daga mutum kuwa sun kasu zuwa gida biyu abisa la’akari da nau’insu. Kodai wanda mutum ya ke yi tsakaninsa da mahaliccinsa ko kuma wadanda ya ke yi wa ‘yan’uwansa na halitta.

 Dangane da nau’in farko, musulunci ya sha banban da addinin kiristanci a hanyar samun gafara. Mai laifi baya da bukatar ya zauna a gaban malamin addini domin ya yi furuci da munanan ayyukan da ya yi bayan an yi masa Baptisma. Kuma musulmi baya da bukatar ya rubuta littafin tarihin rayuwarsa a ciki har ya ambaci zunuban da ya aikata tsakaninsa da mahaliccinsa kamar yadda jean jacques rousseau ya yi acikin littafinsa na Confession. Ko kuma kamar yadda  malamin darikar Roman Katolika Waliyi  Augustine Na Hippo ya yi  acikin littafinsa mai wannan irin taken.
      
 Abinda mutum ya ke da bukatuwa da shi domin ya kankare nau’in farko na laifukansa shi ne ya nemi gafara kai tsaye daga  mahaliccinsa cikin rufin asiri ba tare da wani ya ji ba. Matukar kuwa ba tara Allah da wani mahaluki  ya  yi ba a bauta, to ko da   girman zunubansa sun kai tudun Dala da Goron Dutse, matukar ya cika sharuddan tuba kamar yadda su ka zo acikin nassin addini Allah zai yi masa gafara. Domin kuwa shi Allah  ma’abocin gafara ne  da kuma rahama. Kuma babu abinda zai yi da azabtar da mutane idan su ka yi masa godiya, kuma su ka yi imani.

Nau’i na biyu na laifin da mutum ya ke iya  yi wa dan’uwansa mutum,  shi ne abinda  tsofaffin gwamnoni biyu  na Gombe da Borno da kuma mai ci a yanzu a Bauchi su ka yi furuci da aikatawa akan ‘yan kungiyar  Jama’atu Ahlusuna Lidda’awa Wal jihad, har kuma suka nemi gafararsu.!

 Shakka babu wannan matsayin na gwamnonin uku wani abu ne da ya kamata ya faru tun tuni ba sai yanzu ba. Domin kuwa ko pol pot da ya gina daularsa da kokunan kawunan mutane a Cambodia  http://www.pbase.com/bygaspo/image/40246135   Idan ya ga kisan gillar da aka yi wa ‘yan kungiyar da ake kira Boko Haram zai  karbi wandanda su ke da hannu a kisan a matsayin kwamandoji a rundunarsa. Balle kuma ace ya ga yadda aka baje gawawwakinsu bayan kisan wulakanci kamar ba ‘ya’yan mutum mai daraja ba, a raye ya ke ko a mace. http://www.youtube.com/watch?v=3z2I_Px5Klg&feature=related

Abu ne kuma da babu shakku acikinsa cewa salon kisan da aka yi wa ‘yan kungiyar  Ahlusunna Lidda’awa wal jihad, ya jawo musu tausawaya daga mutane da dama a arewacin Njeriya. Da dama daga cikin wadanda su ka soki ‘ya’yan wannan kungiya saboda daukar makamin da su ka yi, sun sake yin nazari bayan da su ka ga hoton kisan gillar da aka yi wa shugabanta  Muhammad Yusuf da aka kama shi da raye. http://www.youtube.com/watch?v=ePpUvfTXY7w

 Abinda ya kara munin laifukan da  gwamnatin Umaru “Yar adua ta tafka shi ne nuna banbanci a  mu’amala da kungiyoyin Niger-Delta masu dauke da makami. Kai kace wadancan ‘yan kasa ne su kuma  ‘yan kungiyar  Ahlusunna  lidda’awa Wal jihad abokan gaba ne da su ka kawowa tarayyar Najeriya hari daga waje.

Watakila ‘yan siyasar da su ka baiwa jami’an tsaro umarnin aikata waccan  ta’asar sun tsammaci cewa hakan ne zai kawo  karshen waccan kungiya.  Sun kuma zaci cewa zai cusa tsoro acikin zuciyar duk wanda ya ke mafarkin shiga cikinta daga baya.

Sai dai bayan kasa da shekara guda da yakin ya isa birnin Abuja  kuma cikin babbar cibiyar ‘yan sanda da kuma batakashin da ya ke ci gaba da furuwa yanzu a jahohin Borno da Bauchi, dokokin wasa sun sauya.

Abin tambaya anan shi ne menene ya sa wadannan gwamnonin uku su ka nemi gafarar ‘yan kungiyar Ahlussunna Lidda’awa Wal Jihad a wannan lokacin?

Dalilan da su ke ingiza mutum ya yi furuci da cutar da dan’uwansa mutum sannan kuma har ya nemi gafararsa ba su wuce dayan biyu. Kodai sukar lamiri ko kuma matsin lamba  na wani abu mai karfi daga waje wanda zai iya daukar salo daban-daban.

 Ma’anar lamiri  (Larabci: Wujdan, Ingilishi: Conscience) shi ne  mizanin da ya ke tare da kowane mutum wanda shi ne ya ke auna dukkanin ayyukan da su ke bijirowa daga gare shi masu kyau ko munana. Idan mutum ya aikata abinda ya ke daidai zai fada masa, idan kuma ya yi mummuna zai fada masa. Immanuel Kant (  1724 -1804)  ya kafa dalilin samuwar Ubangiji ta hanyar  wannan mizanin na sanin daidai da kuskure wanda  ya ke tare da kowane mutum, a cikin littafinsa na  Critique of Pure Reason. Ya kuwa banbanta shi da hankali ta hanyar cewa shi lamiri bai san maslaha wajen yanke hukunci ga aikin da mutum ya aikata na kwarai ko kummuna ba. Hanaklin mutum ne ya ke fada masa ya yi karya saboda ya kare wata manufa tashi, shi kuma lamiri zai fada masa cewa karya ba ta da kyau. Shi ne kuma ya ke fadawa mutum cewa kada ya yi zalunci domin zalunci ba abu ne mai kyau ba, ba kuma saboda wata maslaha da mutum zai iya amfanuwa da ita ba idan bai yi zaluncin ba. Wannan lamirin shi ne ya ke sa mutum jin nadama bayan ya gama  shan romon wani laifi da ya aikata.

Sabanin nazariyyar da ta ke cewa al’ummar da mutum ya bude ido da girma acikinta ce ta  ke yi masa cushen abubuwa masu kyau da marasa kyau, Immanuel Kant ya yi imani da cewa ana haihuwar mutum ne da lamirinsa.  Kuma kyawawan abubuwa da munana  sakakku ne masu zaman kansu, suna kuma da siffa ta gama-gari. Wannan fahimta ta Immanuel Kant akan lamiri daidai ta ke da fadin kur’ani mai girma cewa:

“ Rantsuwa da rayi- na dan’adam- da  wanda ya daidaita ta-a halitta.”
“Kuma ya kimtsa mata fajircinta da kuma tsoron Allah.”          ( jawabin rantsuwa)
                                                                    (Suratu shams: 6-7)


 Lamiri a cikin adabi na musulunci  yana zuwa da ma’anar rayi, nafs,  kuma kur’ani ya ambace shi da  halaye guda uku ba tare da kari ko ragi ba. Na farko shi ne wanda ya ke zungurin mutum yana fada masa abubuwa  marasa kyau da ya ke aikatawa, wanda ya kira da sunan Nafs al-Lawwama.   Shi ne dan sako na farko daga Ubangiji zuwa ga mutum kafin annabawa da saukakkun littatafai. Ubangijin da ya halicci mutum ya yi rantsuwa da wannan lamirin saboda girman matsayinsa.
 
“Ina rantsuwa da ranar alkiyama.”
Ina kuma rantsuwa da rai mai yawan zargin mai ita.”
                                                              (suratul kiyama: 1-2)

Wannan shi ne ka’ida da tushe na halin lamarin  kowane mutum.  Wananan halin ne a tsakiya sauran biyun kuwa suna hagu da damarsa.  Shi ne kuma mararrabar hanya wacce lamiri ya ke baiwa mutum zabi, idan ya ga dama ya  taka matakalan da zai yi sama zuwa ga daukaka ta hanyar  yawaita ayyukan kwarai, ko kuma ya fadi  ya ci kasa  ta hanyar yawaita munanan ayyuka. Na biyu shi ne kur’ani ya ke kira rayin da ta sami nutsuwa acikin ayyukan kwarai, Nasf mutma’innah.

Ya ke wannan rai wacce ta sami nutuswa.”                                                                        
                                                (suratul Fajr: 10)


                                                                          
Hali na uku  na lamirin mutum shi ne wanda ya ke umartarsa da aikata laifuna, wato nafsul ammarah.


“Hakika rai, mai yawan umarni ne da mummunan aiki sai wanda Ubangijina ya ji kansa.”
                                                        (Suratu Ysuf: 52:)

Wanda ya amsa kiran lamirinsa zuwa yin aiki na kwarai shi ne wanda ya rabauta. Wanda kuma ya amsa kira zuwa ga munanan ayyuka shi ne tababbe. Wannan ma’anar ce ta zo cikin  kur’ani da cewa:

“Wanda ya tsarkake ta ( daga laifuka) , ya rabauta.”
“Wanda kuma ya gurbatata ( da laifuka)  ya tabe.”
                                                       (suratu shams: 9-10)

 Babban malamin addinin Kirista a karni na goma sha uku St Thomas Aquinas a cikin karamin littafinsa na dokar dabi’a                         ( Natural Law) ya ce: “Lamiri baiwa ce daga Ubangiji da ta ke sa mutum ya dauki matakin da ya dace.”

Kuma a bisa fahimtar Immanuel Kant, lamarin mutum baya fasa fada masa matsayin kowane aiki da ya bijiro daga gare shi, mai kyau ne ko mummuna.  Kuma akan wannan ka’idar ta ci gaba da aikin lamiri babu kakkautawa wajen yanke hukunci akan ayyukan mutum wani sashe na masana halayyar dan’adam su ka fito da ka’idar nan ta   “Azabar lamiri”  “ma’anarsa kuwa shi ne shiga cikin azabar ruhi da mai yawan aikata maifuka  ya ke samun kansa aciki, musamman idan ya shafi cutar da ‘yan’uwansa mutane.

Idan kuwa laifukan da mutum ya ke aikatawa na cutar da mutane sun yawaita, to azabar da lamirinsa ya  zai shiga ciki za ta iya ingiza shi zuwa ga haukacewa. A rayuwa ta hakika hakan yana faruwa da mutane da dama. Shi ne kuma abinda malam bahaushe ya baiwa sunan alhaki. Ya kuma kirkiro karin magana akansa da ya ke cewa:  “Alhaki kuikuyo ne mai shi ya ke bi.”

 Sau da yawa wasu masu aikata laifuka suna yin furuci da munanan ayyukansu a lokacin da su ke kan gadon mutuwa.

Tabbas kamun alhaki a wurin malam bahaushe yana da fuskoki guda biyu. Kodai wani bala’i na zahiri ya fada kan wanda ya cutar da wani, ko kuma na ba’dini kamar hauka.

Adabi mai yaye labulen rayuwa ( interpretive literature ), ba adabin nishadi da kasuwanci ba( Escape Literature) acike ya ke da misalai akan yadda aikata laifi ya ke  ingiza mutum zuwa ga hauka. Watakila babu wani misali akan wannan batu da ya kai littafin “Cirme And Punishment “ Na Fyodor Destoevsky.  Jarumin wannan labarin  Raskolnikov  ya halartawa kansa kashe tsohuwar mace  bisa manufa ta koli wacce ita ce samun kudinta da zai yi ayyukan alheri da su. A matsayinsa na tsohon dabilin jami’a a fagen shari’a ya iya kaucewa barin duk wani dalili na zahiri da jami’an tsaro ko kotu za su yi amfani da su domin hukunta shi.  Sai dai lamirinsa  ya ci gaba da zungurinsa, a karhse kuma ya zama mahaukaci, wanda shi ne sakamakon laifin da ya aikata.

Idan mu ka koma kan gwamnoni uku da su ka nemi gafara akan laifukan da su ka yi wa ‘yan kungiyar  Ahlusunna Lidda’wa Wal jihad za mu yi tambaya kamar haka?

Shin wannan ne kadai laifin da su ka aikata a tsawon lokacin mulkinsu saboda haka lamirinsu ya zungure su, su ka nemi gafara akansa shi kadai?

Watakila idan ba wanda ya samu biyan bukatar maslahar kashin kansa ta abin duniya da mukami ba, babu wanda zai raba daya biyu akan cewa, gwamnonin Borno da Bauchi da Gombe sun cutar da al’ummun jahohinsu ta fuskoki da dama a tsawon lokacin aikinsu., kamar sauran gwamnonin tarayyar Najeriya.

Shakka babu da dakwai wani dalili na daban acikin lamirinsu da kuma wajensa da ya ingiza su su ka nemi gafarar ‘yan kungiyar Ahlusnnan Lidda’aw Wal jihad.

Wannan shi ne abinda bangare na biyu na wannan kasida zai bijiro da shi..

Ustazai da shehunai su bani uzuri ba wa’azin addini wannan kasida ta ke yi ba, sharhin halin dan’adam ne  dangane da aikata laifi da kuma neman gafara jigonta.



No comments:

Post a Comment