Sunday, June 26, 2011

Ranar Fada Da Muggan Kwayoyi Ta Duniya ( Gaba ko Baya) ?

26/6/2011

A yau, 26 ga watan yuni ne ake cika shekaru 24 daidai da babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da baiwa wannan ranar sunan ta fada da muggan kwayoyi da kuma fataucinsu a duniya. A kowace shekara kuwa ana gudanar da taruka da  nufin wayar da kan mutane akan hatsarin da ya ke tattare da amfani da muggan kwayoyi sannan kuma a jawo hankalin gwamnatoci akan su sake zage damtse wajen fada da masu fataucinta.

 Kafin shekarar 1987  da aka zabi radawa wata rana guda sunan ta fada da muggan kwayoyi, an sha yin taruka da kulla yarjeniyoyi akan yadda za a fuskanci wannan matsala. Watakila daya daga cikin yarjejeniya mafi shahara ita ce ta 1961 da mafi yawancin kasashen duniya su ka halarta  su ka amince da kudurorin da majalisar dinkin duniya ta amince da su na musayar bayanai a tsakaninsu.

Su dai muggan kwayoyi suna kunshe da sanadarorin kimiyya wadanda idan mutum ya yi amfani da su za su hargitsa yadda kwakwalwarsa ta ke aiki.  Za su kuma fitar da ita daga halinta na dabi’a zuwa wani hali na dabanin. Haka nan kuma suna yin illa ga yadda  jikin mutum ya kamata ya gudanar da aikinsa. Wanda a karshe hakan ya ke shafar ci gaban al’umma.


 Bisa la’akari da tasirin muggan kwayoyi ga kwakwalwa da jikin mutum, za a iya kasa su zuwa gida hudu.

 1-Masu  kashe jiki (depressants):
Nau’in wadannan kwayoyin sun hada da Heroine da opium da Morphine. 

Tasirinsu ya hada da rage saurin aikin kwakwalwa da rage saurin  bugun zuciya da kuma lumfashi  da rage karfin bugawar jini sannan su sanya bacci.

2-Masu sa kuzari (stimulants):

Nau’insu  ya kunshi Cocaine da nicotine.

Tasirinsu ya kunshi sanya kuzari da kara karfin bugawar zuciya da lumfashi da bugawar jini sannan kuma da hana bacci da rage sha’awar cin abinci.

3-  Masu sa Sambatu: (Hallucinogen)

Nau’insu wadannan kwayoyi ya kunshi PCP da LSD.

Tasirinsu: Kamar yadda madubin da ya ke yin zagi yana nuna hotunan abubuwa a gurbace, haka nana gabobin ji da gani na jikin mutum su ke yin zagi idan ya yi amfani da wannan nau’in na kwayoyi. Mutum zai rika ganin abinda ya ke gabansa da wata sura ta daban ba tashi ta hakika ba. Ko ya ya rika jin magana da wani salo na daban wanda ya sabawa hakikanin abinda ake fada. Ko ya rika sawwara wasu abubuwa acikin zuciyarsa da ba gaskiya ba ne.

4-Wadanda ake shaka ko zuka (inhalants)

Nau’in wannan kwaya shi ne tabar wiwi ko shalisho.

Tasirinsu kuwa ya hada da bugun zuciya da karfi kuma kan mutum zai yi nauyi ko kuma ciwo sannan kuma kwakwalwa ta zama mai nawar maida martani.

Kwayoyin da ake sha suna daukar minti 20 zuwa minti 30 sannan illarsu ta fara.

Wadanda ake shigar da su cikin jijiyoyi ta hanyar allura suna daukar dakikoki 20 zuwa 30 kafin su fara illata jiki.

Wadanda ake shigar da su ta hanyar jijiyoyin damatsa suna daukar dakikoki 3 zuwa biyar su fara sakin gubar da ta ke tattare da su ga mutum.

Wadanda ake shaka kuwa suna daukar dakikoki 3 zuwa biyar su fara barna ga mutum.

Kwakwalwa ita ce zakarin dafin farko da muggan kwayoyi su ke yi wa illloli. Baya ga rage karfin aikin wasu sassa nata, tana kuma yin sabo da kamuwa da su da maida mutum ya zama tamkar bawa. Sakamakon wannan zai iya zama rabuwa da cikakken hankali.

Gangar jikin mutum kuwa yana rasa kwayoyin halittar da ya ke bukata domin su rika ba shi kariya a lokacin da kwayoyin cuta su ka kai masa hari. Wannan zai maida shi mai kamuwa da cutuka da dama fiye da wanda muggan kwayoyi ba su yi masa illa ba. Bugu da kari muggan kwayoyi suna rage daidaiton da ya ke tsakanin sanadarori daban-daban na jikin mutum.

Abin takaici ne cewa har yanzu babu alamun nasara wajen kawo karshen wannan annoba a duniya.  Baya ga karuwar da masu shan muggan kwayoyi su ke yi saboda da dalilai da dama, su ma kungiyoyin da su ke hada-hadarsu suna kara karfi. Ba da jimawa ba kwamitin musamman na kasa da kasa wanda ya kunshi tsohon magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Kofi Anan su ka sanar da cewa hanyoyin da ake amfani da sun kasa kawo karshen matsalar muggan kwayoyi.

A cikin yankin Afrika ta yamma kungiyoyin da su ke hada-hadar muggan kwayoyi suna kara karfi. Wannan yankin ya zama hanya mafi girma ta jigilar muggan kwayoyi zuwa nahiyar turai acikin shekarun bayan nan. A bisa rahoton  ofishin Majalisar Dinkin Duniya a  wannan yankin, hada-hadar muggan kwayoyin da ake yi ta kai dalar Amurka miliyan 800 a kowace shekara. Bugu da kari ana kuma samun karuwar mutanen wannan yankin da su ke shiga cikin hada-hadar muggan kwayoyi.

Watakila fada da wannan matsalar da ake yi ta fuskar tsaro ne kadai ya sa ba a ganin sakamakon da ya dace.  Da kuma maida hankali akan masu hada-hadarta fiye da yadda ake maida hankali akan masu shanta da magance matsalolin daga tushe. Dukkanin dalilan da su ke tura mutane shan muggan kwayoyi ne ya kamata a maida hankali wajen magance su.Wannan kuwa yana bukatuwa da dabaru daban-daban da su ka sha gaban batun tsaro kadai.
 Idan  kuwa masu  fataucin muggan kwayoyi  su ka rasa kasuwar da za su sayar da hajarsu to karfin da su ke da shi zai ragu.

No comments:

Post a Comment