Friday, July 8, 2011

Neman Gafarar Gwamnoni Uku Ga Boko Haram. (Tsakanin Sukar Lamiri Da Rusunawa Ga Karfi.)



                     Neman Gafarar Gwamnoni Uku Ga Boko Haram.

                                    Tsakanin Sukar Lamiri Da Rusunawa Ga Karfi.

                                                              (1-2)

                                                         Mujtaba Adam.
                                             nigeria3000@yahoo.com

8/7/2011


Yanzu duk shakiyyan birni sun fadi…. Ba tsoron Allah su ke ba, amma tsoron yari su ke yi. Saboda Allah na musu lamuni… yari ba ya bari sai can gaba.”
                                            
                           Ali Dan Sarki: Wakar Yarin Usumanu Nagoggo.


   (1)           


“Yin furuci da kuskure” kamar yadda Dmitri Fyodorovich, ya fadawa dan’uwansa Alyosha a cikin littafin Brothers Karamazov, “Abu ne mai tsarki.”  Wannan tsarkin na yin furuci da kuskure sannan  kuma da neman gafara akansa, ya samo asali ne daga kasantuwarsa wata kima ta ‘‘yan’adamtaka da addini da kuma lafiyayyen hankali.


Laifukan da su ke bijirowa daga mutum kuwa sun kasu zuwa gida biyu abisa la’akari da nau’insu. Kodai wanda mutum ya ke yi tsakaninsa da mahaliccinsa ko kuma wadanda ya ke yi wa ‘yan’uwansa na halitta.

 Dangane da nau’in farko, musulunci ya sha banban da addinin kiristanci a hanyar samun gafara. Mai laifi baya da bukatar ya zauna a gaban malamin addini domin ya yi furuci da munanan ayyukan da ya yi bayan an yi masa Baptisma. Kuma musulmi baya da bukatar ya rubuta littafin tarihin rayuwarsa a ciki har ya ambaci zunuban da ya aikata tsakaninsa da mahaliccinsa kamar yadda jean jacques rousseau ya yi acikin littafinsa na Confession. Ko kuma kamar yadda  malamin darikar Roman Katolika Waliyi  Augustine Na Hippo ya yi  acikin littafinsa mai wannan irin taken.
      
 Abinda mutum ya ke da bukatuwa da shi domin ya kankare nau’in farko na laifukansa shi ne ya nemi gafara kai tsaye daga  mahaliccinsa cikin rufin asiri ba tare da wani ya ji ba. Matukar kuwa ba tara Allah da wani mahaluki  ya  yi ba a bauta, to ko da   girman zunubansa sun kai tudun Dala da Goron Dutse, matukar ya cika sharuddan tuba kamar yadda su ka zo acikin nassin addini Allah zai yi masa gafara. Domin kuwa shi Allah  ma’abocin gafara ne  da kuma rahama. Kuma babu abinda zai yi da azabtar da mutane idan su ka yi masa godiya, kuma su ka yi imani.

Nau’i na biyu na laifin da mutum ya ke iya  yi wa dan’uwansa mutum,  shi ne abinda  tsofaffin gwamnoni biyu  na Gombe da Borno da kuma mai ci a yanzu a Bauchi su ka yi furuci da aikatawa akan ‘yan kungiyar  Jama’atu Ahlusuna Lidda’awa Wal jihad, har kuma suka nemi gafararsu.!

 Shakka babu wannan matsayin na gwamnonin uku wani abu ne da ya kamata ya faru tun tuni ba sai yanzu ba. Domin kuwa ko pol pot da ya gina daularsa da kokunan kawunan mutane a Cambodia  http://www.pbase.com/bygaspo/image/40246135   Idan ya ga kisan gillar da aka yi wa ‘yan kungiyar da ake kira Boko Haram zai  karbi wandanda su ke da hannu a kisan a matsayin kwamandoji a rundunarsa. Balle kuma ace ya ga yadda aka baje gawawwakinsu bayan kisan wulakanci kamar ba ‘ya’yan mutum mai daraja ba, a raye ya ke ko a mace. http://www.youtube.com/watch?v=3z2I_Px5Klg&feature=related

Abu ne kuma da babu shakku acikinsa cewa salon kisan da aka yi wa ‘yan kungiyar  Ahlusunna Lidda’awa wal jihad, ya jawo musu tausawaya daga mutane da dama a arewacin Njeriya. Da dama daga cikin wadanda su ka soki ‘ya’yan wannan kungiya saboda daukar makamin da su ka yi, sun sake yin nazari bayan da su ka ga hoton kisan gillar da aka yi wa shugabanta  Muhammad Yusuf da aka kama shi da raye. http://www.youtube.com/watch?v=ePpUvfTXY7w

 Abinda ya kara munin laifukan da  gwamnatin Umaru “Yar adua ta tafka shi ne nuna banbanci a  mu’amala da kungiyoyin Niger-Delta masu dauke da makami. Kai kace wadancan ‘yan kasa ne su kuma  ‘yan kungiyar  Ahlusunna  lidda’awa Wal jihad abokan gaba ne da su ka kawowa tarayyar Najeriya hari daga waje.

Watakila ‘yan siyasar da su ka baiwa jami’an tsaro umarnin aikata waccan  ta’asar sun tsammaci cewa hakan ne zai kawo  karshen waccan kungiya.  Sun kuma zaci cewa zai cusa tsoro acikin zuciyar duk wanda ya ke mafarkin shiga cikinta daga baya.

Sai dai bayan kasa da shekara guda da yakin ya isa birnin Abuja  kuma cikin babbar cibiyar ‘yan sanda da kuma batakashin da ya ke ci gaba da furuwa yanzu a jahohin Borno da Bauchi, dokokin wasa sun sauya.

Abin tambaya anan shi ne menene ya sa wadannan gwamnonin uku su ka nemi gafarar ‘yan kungiyar Ahlussunna Lidda’awa Wal Jihad a wannan lokacin?

Dalilan da su ke ingiza mutum ya yi furuci da cutar da dan’uwansa mutum sannan kuma har ya nemi gafararsa ba su wuce dayan biyu. Kodai sukar lamiri ko kuma matsin lamba  na wani abu mai karfi daga waje wanda zai iya daukar salo daban-daban.

 Ma’anar lamiri  (Larabci: Wujdan, Ingilishi: Conscience) shi ne  mizanin da ya ke tare da kowane mutum wanda shi ne ya ke auna dukkanin ayyukan da su ke bijirowa daga gare shi masu kyau ko munana. Idan mutum ya aikata abinda ya ke daidai zai fada masa, idan kuma ya yi mummuna zai fada masa. Immanuel Kant (  1724 -1804)  ya kafa dalilin samuwar Ubangiji ta hanyar  wannan mizanin na sanin daidai da kuskure wanda  ya ke tare da kowane mutum, a cikin littafinsa na  Critique of Pure Reason. Ya kuwa banbanta shi da hankali ta hanyar cewa shi lamiri bai san maslaha wajen yanke hukunci ga aikin da mutum ya aikata na kwarai ko kummuna ba. Hanaklin mutum ne ya ke fada masa ya yi karya saboda ya kare wata manufa tashi, shi kuma lamiri zai fada masa cewa karya ba ta da kyau. Shi ne kuma ya ke fadawa mutum cewa kada ya yi zalunci domin zalunci ba abu ne mai kyau ba, ba kuma saboda wata maslaha da mutum zai iya amfanuwa da ita ba idan bai yi zaluncin ba. Wannan lamirin shi ne ya ke sa mutum jin nadama bayan ya gama  shan romon wani laifi da ya aikata.

Sabanin nazariyyar da ta ke cewa al’ummar da mutum ya bude ido da girma acikinta ce ta  ke yi masa cushen abubuwa masu kyau da marasa kyau, Immanuel Kant ya yi imani da cewa ana haihuwar mutum ne da lamirinsa.  Kuma kyawawan abubuwa da munana  sakakku ne masu zaman kansu, suna kuma da siffa ta gama-gari. Wannan fahimta ta Immanuel Kant akan lamiri daidai ta ke da fadin kur’ani mai girma cewa:

“ Rantsuwa da rayi- na dan’adam- da  wanda ya daidaita ta-a halitta.”
“Kuma ya kimtsa mata fajircinta da kuma tsoron Allah.”          ( jawabin rantsuwa)
                                                                    (Suratu shams: 6-7)


 Lamiri a cikin adabi na musulunci  yana zuwa da ma’anar rayi, nafs,  kuma kur’ani ya ambace shi da  halaye guda uku ba tare da kari ko ragi ba. Na farko shi ne wanda ya ke zungurin mutum yana fada masa abubuwa  marasa kyau da ya ke aikatawa, wanda ya kira da sunan Nafs al-Lawwama.   Shi ne dan sako na farko daga Ubangiji zuwa ga mutum kafin annabawa da saukakkun littatafai. Ubangijin da ya halicci mutum ya yi rantsuwa da wannan lamirin saboda girman matsayinsa.
 
“Ina rantsuwa da ranar alkiyama.”
Ina kuma rantsuwa da rai mai yawan zargin mai ita.”
                                                              (suratul kiyama: 1-2)

Wannan shi ne ka’ida da tushe na halin lamarin  kowane mutum.  Wananan halin ne a tsakiya sauran biyun kuwa suna hagu da damarsa.  Shi ne kuma mararrabar hanya wacce lamiri ya ke baiwa mutum zabi, idan ya ga dama ya  taka matakalan da zai yi sama zuwa ga daukaka ta hanyar  yawaita ayyukan kwarai, ko kuma ya fadi  ya ci kasa  ta hanyar yawaita munanan ayyuka. Na biyu shi ne kur’ani ya ke kira rayin da ta sami nutsuwa acikin ayyukan kwarai, Nasf mutma’innah.

Ya ke wannan rai wacce ta sami nutuswa.”                                                                        
                                                (suratul Fajr: 10)


                                                                          
Hali na uku  na lamirin mutum shi ne wanda ya ke umartarsa da aikata laifuna, wato nafsul ammarah.


“Hakika rai, mai yawan umarni ne da mummunan aiki sai wanda Ubangijina ya ji kansa.”
                                                        (Suratu Ysuf: 52:)

Wanda ya amsa kiran lamirinsa zuwa yin aiki na kwarai shi ne wanda ya rabauta. Wanda kuma ya amsa kira zuwa ga munanan ayyuka shi ne tababbe. Wannan ma’anar ce ta zo cikin  kur’ani da cewa:

“Wanda ya tsarkake ta ( daga laifuka) , ya rabauta.”
“Wanda kuma ya gurbatata ( da laifuka)  ya tabe.”
                                                       (suratu shams: 9-10)

 Babban malamin addinin Kirista a karni na goma sha uku St Thomas Aquinas a cikin karamin littafinsa na dokar dabi’a                         ( Natural Law) ya ce: “Lamiri baiwa ce daga Ubangiji da ta ke sa mutum ya dauki matakin da ya dace.”

Kuma a bisa fahimtar Immanuel Kant, lamarin mutum baya fasa fada masa matsayin kowane aiki da ya bijiro daga gare shi, mai kyau ne ko mummuna.  Kuma akan wannan ka’idar ta ci gaba da aikin lamiri babu kakkautawa wajen yanke hukunci akan ayyukan mutum wani sashe na masana halayyar dan’adam su ka fito da ka’idar nan ta   “Azabar lamiri”  “ma’anarsa kuwa shi ne shiga cikin azabar ruhi da mai yawan aikata maifuka  ya ke samun kansa aciki, musamman idan ya shafi cutar da ‘yan’uwansa mutane.

Idan kuwa laifukan da mutum ya ke aikatawa na cutar da mutane sun yawaita, to azabar da lamirinsa ya  zai shiga ciki za ta iya ingiza shi zuwa ga haukacewa. A rayuwa ta hakika hakan yana faruwa da mutane da dama. Shi ne kuma abinda malam bahaushe ya baiwa sunan alhaki. Ya kuma kirkiro karin magana akansa da ya ke cewa:  “Alhaki kuikuyo ne mai shi ya ke bi.”

 Sau da yawa wasu masu aikata laifuka suna yin furuci da munanan ayyukansu a lokacin da su ke kan gadon mutuwa.

Tabbas kamun alhaki a wurin malam bahaushe yana da fuskoki guda biyu. Kodai wani bala’i na zahiri ya fada kan wanda ya cutar da wani, ko kuma na ba’dini kamar hauka.

Adabi mai yaye labulen rayuwa ( interpretive literature ), ba adabin nishadi da kasuwanci ba( Escape Literature) acike ya ke da misalai akan yadda aikata laifi ya ke  ingiza mutum zuwa ga hauka. Watakila babu wani misali akan wannan batu da ya kai littafin “Cirme And Punishment “ Na Fyodor Destoevsky.  Jarumin wannan labarin  Raskolnikov  ya halartawa kansa kashe tsohuwar mace  bisa manufa ta koli wacce ita ce samun kudinta da zai yi ayyukan alheri da su. A matsayinsa na tsohon dabilin jami’a a fagen shari’a ya iya kaucewa barin duk wani dalili na zahiri da jami’an tsaro ko kotu za su yi amfani da su domin hukunta shi.  Sai dai lamirinsa  ya ci gaba da zungurinsa, a karhse kuma ya zama mahaukaci, wanda shi ne sakamakon laifin da ya aikata.

Idan mu ka koma kan gwamnoni uku da su ka nemi gafara akan laifukan da su ka yi wa ‘yan kungiyar  Ahlusunna Lidda’wa Wal jihad za mu yi tambaya kamar haka?

Shin wannan ne kadai laifin da su ka aikata a tsawon lokacin mulkinsu saboda haka lamirinsu ya zungure su, su ka nemi gafara akansa shi kadai?

Watakila idan ba wanda ya samu biyan bukatar maslahar kashin kansa ta abin duniya da mukami ba, babu wanda zai raba daya biyu akan cewa, gwamnonin Borno da Bauchi da Gombe sun cutar da al’ummun jahohinsu ta fuskoki da dama a tsawon lokacin aikinsu., kamar sauran gwamnonin tarayyar Najeriya.

Shakka babu da dakwai wani dalili na daban acikin lamirinsu da kuma wajensa da ya ingiza su su ka nemi gafarar ‘yan kungiyar Ahlusnnan Lidda’aw Wal jihad.

Wannan shi ne abinda bangare na biyu na wannan kasida zai bijiro da shi..

Ustazai da shehunai su bani uzuri ba wa’azin addini wannan kasida ta ke yi ba, sharhin halin dan’adam ne  dangane da aikata laifi da kuma neman gafara jigonta.



Sunday, June 26, 2011

Ranar Fada Da Muggan Kwayoyi Ta Duniya ( Gaba ko Baya) ?

26/6/2011

A yau, 26 ga watan yuni ne ake cika shekaru 24 daidai da babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da baiwa wannan ranar sunan ta fada da muggan kwayoyi da kuma fataucinsu a duniya. A kowace shekara kuwa ana gudanar da taruka da  nufin wayar da kan mutane akan hatsarin da ya ke tattare da amfani da muggan kwayoyi sannan kuma a jawo hankalin gwamnatoci akan su sake zage damtse wajen fada da masu fataucinta.

 Kafin shekarar 1987  da aka zabi radawa wata rana guda sunan ta fada da muggan kwayoyi, an sha yin taruka da kulla yarjeniyoyi akan yadda za a fuskanci wannan matsala. Watakila daya daga cikin yarjejeniya mafi shahara ita ce ta 1961 da mafi yawancin kasashen duniya su ka halarta  su ka amince da kudurorin da majalisar dinkin duniya ta amince da su na musayar bayanai a tsakaninsu.

Su dai muggan kwayoyi suna kunshe da sanadarorin kimiyya wadanda idan mutum ya yi amfani da su za su hargitsa yadda kwakwalwarsa ta ke aiki.  Za su kuma fitar da ita daga halinta na dabi’a zuwa wani hali na dabanin. Haka nan kuma suna yin illa ga yadda  jikin mutum ya kamata ya gudanar da aikinsa. Wanda a karshe hakan ya ke shafar ci gaban al’umma.


 Bisa la’akari da tasirin muggan kwayoyi ga kwakwalwa da jikin mutum, za a iya kasa su zuwa gida hudu.

 1-Masu  kashe jiki (depressants):
Nau’in wadannan kwayoyin sun hada da Heroine da opium da Morphine. 

Tasirinsu ya hada da rage saurin aikin kwakwalwa da rage saurin  bugun zuciya da kuma lumfashi  da rage karfin bugawar jini sannan su sanya bacci.

2-Masu sa kuzari (stimulants):

Nau’insu  ya kunshi Cocaine da nicotine.

Tasirinsu ya kunshi sanya kuzari da kara karfin bugawar zuciya da lumfashi da bugawar jini sannan kuma da hana bacci da rage sha’awar cin abinci.

3-  Masu sa Sambatu: (Hallucinogen)

Nau’insu wadannan kwayoyi ya kunshi PCP da LSD.

Tasirinsu: Kamar yadda madubin da ya ke yin zagi yana nuna hotunan abubuwa a gurbace, haka nana gabobin ji da gani na jikin mutum su ke yin zagi idan ya yi amfani da wannan nau’in na kwayoyi. Mutum zai rika ganin abinda ya ke gabansa da wata sura ta daban ba tashi ta hakika ba. Ko ya ya rika jin magana da wani salo na daban wanda ya sabawa hakikanin abinda ake fada. Ko ya rika sawwara wasu abubuwa acikin zuciyarsa da ba gaskiya ba ne.

4-Wadanda ake shaka ko zuka (inhalants)

Nau’in wannan kwaya shi ne tabar wiwi ko shalisho.

Tasirinsu kuwa ya hada da bugun zuciya da karfi kuma kan mutum zai yi nauyi ko kuma ciwo sannan kuma kwakwalwa ta zama mai nawar maida martani.

Kwayoyin da ake sha suna daukar minti 20 zuwa minti 30 sannan illarsu ta fara.

Wadanda ake shigar da su cikin jijiyoyi ta hanyar allura suna daukar dakikoki 20 zuwa 30 kafin su fara illata jiki.

Wadanda ake shigar da su ta hanyar jijiyoyin damatsa suna daukar dakikoki 3 zuwa biyar su fara sakin gubar da ta ke tattare da su ga mutum.

Wadanda ake shaka kuwa suna daukar dakikoki 3 zuwa biyar su fara barna ga mutum.

Kwakwalwa ita ce zakarin dafin farko da muggan kwayoyi su ke yi wa illloli. Baya ga rage karfin aikin wasu sassa nata, tana kuma yin sabo da kamuwa da su da maida mutum ya zama tamkar bawa. Sakamakon wannan zai iya zama rabuwa da cikakken hankali.

Gangar jikin mutum kuwa yana rasa kwayoyin halittar da ya ke bukata domin su rika ba shi kariya a lokacin da kwayoyin cuta su ka kai masa hari. Wannan zai maida shi mai kamuwa da cutuka da dama fiye da wanda muggan kwayoyi ba su yi masa illa ba. Bugu da kari muggan kwayoyi suna rage daidaiton da ya ke tsakanin sanadarori daban-daban na jikin mutum.

Abin takaici ne cewa har yanzu babu alamun nasara wajen kawo karshen wannan annoba a duniya.  Baya ga karuwar da masu shan muggan kwayoyi su ke yi saboda da dalilai da dama, su ma kungiyoyin da su ke hada-hadarsu suna kara karfi. Ba da jimawa ba kwamitin musamman na kasa da kasa wanda ya kunshi tsohon magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Kofi Anan su ka sanar da cewa hanyoyin da ake amfani da sun kasa kawo karshen matsalar muggan kwayoyi.

A cikin yankin Afrika ta yamma kungiyoyin da su ke hada-hadar muggan kwayoyi suna kara karfi. Wannan yankin ya zama hanya mafi girma ta jigilar muggan kwayoyi zuwa nahiyar turai acikin shekarun bayan nan. A bisa rahoton  ofishin Majalisar Dinkin Duniya a  wannan yankin, hada-hadar muggan kwayoyin da ake yi ta kai dalar Amurka miliyan 800 a kowace shekara. Bugu da kari ana kuma samun karuwar mutanen wannan yankin da su ke shiga cikin hada-hadar muggan kwayoyi.

Watakila fada da wannan matsalar da ake yi ta fuskar tsaro ne kadai ya sa ba a ganin sakamakon da ya dace.  Da kuma maida hankali akan masu hada-hadarta fiye da yadda ake maida hankali akan masu shanta da magance matsalolin daga tushe. Dukkanin dalilan da su ke tura mutane shan muggan kwayoyi ne ya kamata a maida hankali wajen magance su.Wannan kuwa yana bukatuwa da dabaru daban-daban da su ka sha gaban batun tsaro kadai.
 Idan  kuwa masu  fataucin muggan kwayoyi  su ka rasa kasuwar da za su sayar da hajarsu to karfin da su ke da shi zai ragu.

Thursday, June 9, 2011

Yan siyasar Arewa.(Kodagai Akan Allon Wasan Dara Na Siyasar Najeriya.)


on Monday, May 17, 2010


Dara, wasa ne da ya ke dogaro da kaifin kwanya ba karfin kwanji ba. Akan allon wannan wasa, kodagan da ake amfani da su a matsayin mayaka suna da yawa. Aikin kowane kodago kuwa shi ne ya toshe duk wata kafa da zai sa a kusanci inda Sarauniya ta ke. Ran Sarauniya ne kadai ya ke da muhimmanci acikin wannan wasa, shi kadai ne abin karewa. Kodago kuwa mayaki ne saboda haka dole ya mutu wajen kare Sarauniya.

Nazariyyar shirya makarkashiya- Consipracy Theory- ba ta burge ni sosai. Ban kuma yi imani da cewa dukkan abinda ya ke faruwa a fagen siyasa makirci ne da ake kitsawa a tsakar dare ba saboda a aiwatar da shi idan gari ya waye. Sai dai wannan bai kore cewa da akwai 'yan siyasa masu kaifin kwakwalwa fiye da wasu ba. Wadanda su ke iya sarrafa 'yanuwansu 'yan siyasa kamar yadda marigayiya Ladi Kwali ta ke sarrafa laka saboda ta kera tukunya ko Randa ko kuma Kwatanniya.

"Yan siyasar arewa manyansu da kananansu kodagai ne da ake amfani da su a matsayin mayaka. Wace saruniya su ke karewa ? shi ne abinda ban sani ba. Sai dai ina da tabbacin cewa wannan Sarauniyar da su ke faduwa daya bayan wajen kare ta ba Daurama ba ce kuma ba Amina ba. Idan kuma na dubi taswirar siyasar Najeriya zan iya bugun kirji in ce Baba Aremu Obasanjo shi ne wanda ya ke kada su hagu da dama domin kare wannan Sarauniyar da na jahilta. Ba ni da shakkun cewa shi kwararren dan wasa ne da ya san abinda ya ke so ya ke kuma aiki tukuru domin cimma manufa.! Ba kuma laifinsa na ke gani ba saboda wannan baiwar da ya ke da ita.! Shekaru kusan goma a baya shugaban Kasar Uganda Yuweri Museveni ya fadi cewa:

"Ba ni ganin laifin turawa da su ka bautar da 'yan Afirka. Wadanda su ka tsaya aka kama su a matsayin bayi ne su ke da laifi."

Lokacin da Obasanjo ya tsaya a cikin birnin katsina ya rantse cewa idan marigayi Umar 'Yar'adua bai zama shugaban kasa ba shi ( Obasanjo) shege ne, mutanen da su ke zagaye da shi sun yi masa tafi. Babu wanda ya kalubalance shi sai lokacin da marigayin ya ke gargarar mutuwa.! A lokacin ne 'yan jarida su ka yi masa tambaya akan cewa zabar Umar da ya yi wani makirci ne da ya kulla domin ya san ba zai yi tsawon rai ba. Shi kuwa ya kare kansa da cewa liktoci sun fada masa cewa cutar da ya ke fama da ita ba za ta hana shi aiki ba.

Na tabbata mafi yawancin mutanen arewa idan ba dukkansu ba sun yi imani da cewa sanin lokacin mutuwar wani mahaluki gaibu ne da makullansa ke hannun Allah. Saboda haka batun Obasanjo ya dora Umar akan karagar mulki saboda idan ya rasu ya sake rike akalar siyasar kasa bai taso ba.! Saukin kan mutanen arewa  ( wanda ba abin yabo ba ne a siyasance) watakila kuma da karfin tasirin gubatacciyar fassarar addini sun rufe musu idanu akan su yi tunanin cewa dora 'Yar'adu'a akan karagar mulki yana da alaka da wasa na siyasa. Ko sun jahilta ko kuma suna sane amma sun rufe idanu cewa a karkashin wasa na siyasa wanda ya kashe abokin hamayyarsa zai iya shiga a yi masa salla jana'iza da shi kuma har ya zubar da hawaye. Tarihin siyasa cike ya ke da misalai irin wadandan da wadanda su ka fi su tayar da hankali.

Sun kuma sakankance cewa tunda dai doka ce ta jam'iyyar P.D.P cewa za a rika karba-karba tsakanin bangarorin kasa to ko bayan Umaru mulki zai ci gaba da zama a hannunsu. Obasanjo ya san cewa a lokacin da mutum ya ke da rauni zai iya mika wuya ga wata doka amma idan ya zama mai karfi ya sa kafa ya ta ke ta. A lokacin da jam'iyyar p.d.p ta yi waccan doka Obasanjo ba shi da iko da karfi saboda haka bai ki amincewa da ita ba. Yanzu da ya zama jan wuya a siyasar Najeriya, wanda kuma ya ke nadawa da saukewa babu abinda zai hana shi sa kafa ya take wannan doka.Wane dan arewa ne zai iya taka masa birki idan ya tsaya kai da fata sai Goodluck Jonathan ya tsaya takara? Ko kuma ya kawo wani wanda zai iya juya shi hagu da dama ya yi wasan kura da shi anan gaba?

Zabar Namadi Sambo a matsayin mataimakin shugaban kasa ya sake tabbatar da cewa wasan kura ake yi da 'yan siyasar arewa. Da kuma ace kungiyoyin arewa na sarakunan gargajiya da fararen hula da dukkan masu bakin fada a ji suna da 'yanci na tunani to da sun ki amincewa da wannan zaben.!. Idan ace wani gwamna ne daga wata jaha ta arewa aka baiwa wannan mukamin to da da sauki.Idan Obasanjo yana da hannu a cikin daukar wannan matakin to shakka babu ya yi wa mutanen arewa bugun mummuke- check mate - a makasa. Bani daga cikin masu cewa an zabe shi ne saboda zai yi saukin juyawa- duk da cewa ban kore hakan ba- amma na san sakamakon da zai biyo baya a kaduna yana da ban tsoro. Dauke Namadi daga kaduna tamkar motsa kodagon dara ne wanda zai jefa sarauniya cikin hatsari. Sarauniyar da na ke nufi anan wacce kuma na sani ita ce zaman lafiya na jahar kaduna.

Wadanda su ke kaduna suna da masaniya akan kwantaccen rikicin addini da kabilancin a cikin wannan jaha da ta ke a matsayin cibiyar arewa. Mutum zai iya bugun kirji ya ce dauke Namadi daga kaduna kada karaurawa ce mai hatsari akan abinda zai biyo baya. Abinda zai faru a lokacin zaben gwamnoni shi ne zai yanke hukunci.

Bani kare siyasar kabilanci da kowace kima, balle in ce dole sai dan arewa ya yi mulki amma ina cikin masu goyon bayan ayi aiki da doka. Idan doka ce rubutacciya ko kuma yarjejeniya koda kuwa ta baka ce akan cewa wannan lokaci ne na mulkin dan arewa to ya kamata 'yan arewan da su ke cikin p.d.p su kare hakkinsu. Ina kuma goyon bayansu akan haka amma ba saboda na yi imani da cewa za su tsinana wani abu ba.! Wanda zai ceto da kasa daga durkushewar da ta ke yi ne abin nema a daidai wannan lokacin mai hatsari ba dan wata kabila ko addini na musamman ba.